(ABNA24.com) Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi watsi da zargin cewa kungiyarsa ce take iko da gwamnatin kasar Labanon.
Sayyeed Hassan Nasarallah ya bayyana haka ne a jiya jumma’a a wani jawabin da yayi kai tsaye ta allunan talbijin a kasar. Ya kuma kara da cewa wadanda suke yada wannan karya, suna nufin tunzura mutanen kasar Lebanon ne kan kungiyar.
Har’ila yau shugaban kungiyar ta Hizbullah Sayyeed Nasarallah ya ce wadanda suke yada wadannan maganganu suna bawa makiyan kasar Lebanon, wadanda suka hada da Amurka da kuma HKI damar shiga cikin lamuran kasar.
Dangane da batun Falasdinwa wadanda gwamnatin kasar Labanon take son hanasu ayyuka a kamfanonin kasar kuma, Sayyeed Nasarallah ya ce an siyasantar da batun, don haka yana kira ga gwamnatin kasar kada da dauki falasdinawa kamar sauran yan kasashen waje da suke kasar, don sauran mutane suna da kasashen su da zasu koma, amma Falasdinawa an mamaye kasarsu don haka ba inda zasu koma.
Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya gabatar da jawabinsa na jiya ne don bikin cika shekara 31 da kafa “Ma’aikatar jihadin Raya kasa “ ta kungiyar.
/129
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi watsi da zargin cewa kungiyarsa ce take iko da gwamnatin kasar Labanon.