(ABNA24.com) Sabon firaministan Birtaniya, Boris Johnson, yayi alkawalin fitar da kasar daga kungiyar tarayya turai a ranar 31 ga watan Oktoba.
Mista Johnson, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan nada shi a wannan matsayin yau Laraba.
A cikin jawabins ana farko a matsayin firaministan na Birtaniya, Johnson, ya ce ba wata makawa zai fitar da kasar daga kungiyar tarayyar turai ba tare da wata wata ba a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa.
A cewarsa zamu mutunta alkawarin da majalisa ta daukar wa al’umma, ko ma ya zata kasancewa, koda ma ba’a cimma yarjejeniya ba, kasarsa shirye take kan hakan..
Yau Laraba ne sabon firamnistan na Birtaniya, B.Johnson, ya isa fadar Buckingham, inda sarauniyar Ingila, Elizabeth, ta damka masa yaunin kafa gwamnati.
Mista B.Johnson dai ya maye gurbin Thereza May, wacce ta yi murabus a kwanakin baya.
/129
25 Yuli 2019 - 06:48
News ID: 964361

Sabon firaministan Birtaniya, Boris Johnson, yayi alkawalin fitar da kasar daga kungiyar tarayya turai a ranar 31 ga watan Oktoba.