23 Yuli 2019 - 04:48
Janar Haj Zadeh: Karyar Trump Akan Harbo Jirgin Sama Maras Matuki Ta Munana

Kwamadan Sojan Sama Na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Ta Iran Ya Ce; Karyar Da Trump Ya Shara ta yi girman da ya jefa mu cikin shakku har mu ka gaskata cewa lallai sun harbo jirginmu na sama maras matuki.!

(ABNA24.com) Kwamadan Sojan Sama Na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Ta Iran Ya Ce; Karyar Da Trump Ya Shara ta yi girman da ya jefa mu cikin shakku har mu ka gaskata cewa lallai sun harbo jirginmu na sama maras matuki.!

Birgediya Janar Ali Haji Zadeh, wanda ya gabatar da jawabi a wurin bayar da horo ga dakarun sojan Sama, ya bayyana cewa: Bayan da Trump ya riya cewa sun harbo jirgin Iran maras matuki, mun gudanar da bincike a bangarori daban-daban na rundunarmu.

Haj Zadeh ya ci gaba da cewa: Girman karyar da Trump din ya shara ya sa mu kanmu mun gaskata cewa; lallai sun harbo mana jirgi. Domin ba mu taba gaskata cewa zai shara karya har haka ba, kuma kai tsaye a kafafen watsa labaru.!

Wannan ne ya sa muka dauki wasu sa’oi gabanin mu karyata labarin,amma a karshe mu ka fahimci cewa jirginmu maras matuki ya gudanar da aikinsa na sintiri akan jirgin ruwan Amurka mai daukar jirage, daga fitarsa har zuwa dawowarsa.



/129