Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, lokacin da ya karbi mambobin Majalisar Ministocinsa da suka kai masa ziyara a fadar gwamnatinsa a birnin Abuja domin taya shi murnar sake lashe kujerar shugabancin kasar a wa’adi na biyu.
Shugaban ya ce, "Ina ganin wa’adina na shekaru hudun karshe, zai yi zafi, mutane na da mantuwa, wannan ne ya sa a lokacin yakin neman zabe, na yi magana akan manyan shirye-shiryenmu " in ji Buhari.
Shugaban ya ce, bai yi kasa a guiwa ba wajen tunatar da al’ummar Najeriya game da alkawuransa na tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arziki da kuma samar da ayyuka ga matasa har ma da yaki da cin hanci da rashawa.
A ranar Larabar da ta gabata ne, Hukumar Zaben Najeriya Mai Zaman Kanta, INEC ta ayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben 2019 bayan ya samu yawan kuri’u fiye da na babban abokin hamayyarsa, Atiuku Abubakar na jam’iyyar PDP.