Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto shugaban yana fadar haka a rubutaccen sakon taya murga ga yan Najeriya musamman kiristoci na zagayowar ranar kirsimeti na wannan shekarar.
Shugaban ya bukaci yan Najeriya su yi fatan cewa wani abin kirki zai fito daga kasarsu musamman idan har an sami hadin kai a tsakaninsu.
Shugaban ya bukaci yan Najeriya su dauki cewa abinda zai zo nan gaba a kasar ya fi alkhairi bisa ga abubuwan da suka gabata.
Buhari ya taya al-ummar Najeriya musamman kiristocin kasar zagayowan ranar haihuwar annabi Isa (a) a garin Bethlaham na kasar Palasdinu shekaru fiye 2000 da suka gabata.
Har'ila yau a cikin sakon, shugaba Buhari ya bayyana irin ci gaban da aka samu a gwamnatinsa cikin shekaru kimani huda da suka gabata, a matsayin ci gaba mai busharan alkhairi nan gaba.
ya ce an sami ci gaba a bangarorin noma da sifiri da manya-manyan ayyukan da sauransu.