An dai hallaka Abou al-Oumarayn ne a cikin hamadar Siriya dake zaman sansani na karshe na kungiyar ta (IS) ko kuma Da'esh.
Wata sanarwa da kakakin kawancen da Amurka ke jagoranta ya fitar dta ce nan gaba za'a fitar da cikakkun bayanai kan kisan babban dan ta'addan.
Abou al-Oumarayn an zarge shi da kisan Peter Kassig, t ahanyar yi masa yankan rago a watan Nuwamba na 2014, bayan sace shi a Siriya a cikin shekara 2013.