Mafi akasarin wadanda aka hallaka matasa ne, kuma mayakan sa kai na kabilar ta Tuareg.
Rahotanni sun ce mayakan jihadin sun kai hare-haren ne har kashi biyu , a kauyukan Awakassa ranar Juma’a da kuma Anderan-Boucane a jiya Asabar.
Gwamnan jihar ya ce akwai yiwuwar mayakan sunyi amfani da rikicin ‘yan kabilar ta Tuareg ne da Fulani wajen samun damar kai harin.
Ci gaba da karuwar hare-haren a Mali dai babbar barazana ce ga shirin gwamnati na gudanar da zaben shugaban kasa, ta sanar da cewa za’a yi a cikin watan Yuli mai zuwa.
29 Afirilu 2018 - 15:17
Lambar labari: 891404
Gwamnan jihar Menaka da ke arewacin Mali Daouda Maiga, ya ce wasu mayaka da ke da’awar Jihadi, sun hallaka ‘yan kabilar Tuareg 40.