Babban kwamadan rundinar, Janar Abdel Amir Yarallah ya fada a cikin wata sanarwa cewa dakarun kasar sun kaddamar da wani gagarimin farmaki yau Laraba don kwato birnin dake yankin Ryad.
Yau kwanaki 13 kenan da dakarun kasar Iraki suka darma damarar yakar 'yan ta'addan a yankunan biyu da suka rage, bayan da suka kwato wasu birane biyu da wasu gomman kauyuka. 288