Yayin tabbatar da hakan yau a garin Maiduguri, kakakin sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman, ya ce Metele, ya fito ne daga bangaren shugabancin kungiyar Boko Haram karkashin Mamman Nur.
Bulama Metele, shi ne mutum na 253, cikin mayakan Boko Haram, da rundunar sojin Najeriya ta yi shelar nemansu ruwa a jallo.
Birgediya Janar Usman ya ce sojin bataliya ta 158 sun kuma kama wasu ‘yan leken asirin kungiyar ta Boko Haram, a kauyukan Kareto da Dangali, kuma bicikensu ya nuna cewa, suna leken asirin ne saboda shirin kai harin ta'addanci kan kauyukan.288