20 Disamba 2016 - 16:14
AL-MILALU WAN NIHAL   Jalsa ta 15(1)

Na Maulana Al-Mujahid Sheikh Hamzah Muhammad Lawal(ama) Yusuf Sulaiman ya rubuta

MU’AWIYAH DAN ABI SUFYAN
A baya mun kawo inda Manzon Allah yake cewa dangane da Mu’awiya : Kar Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya kosar da cikin shi.Muka ce Al-Bulaziriy ya fitar a cikin Ansabul Ashraf.Sannan shi kanshi Mu’awiya yana cewa :
“Hakika addu’an Manzon Allah(sawa) ta riske ni.Kuma ya kasance yana ci a kowane yini sau da yawa a lokuta masu yawa kuma abinci mai yawa”
Kana iya dubawa a cikin As-Siffen da kuma Sahihu Muslim muka ce,a wannan babin da muke so mu darasta wanda suke kafa hujja dashi.
Sannan munce Manzon Allah (sawa) yace dangane da Mu’awiya:
“Amma Mu’awiyah,to shi tantiri ne,bai da dukiya”
Wannan addu’an da Manzon Allah(sawa) yayi akan Mu’awiya na cewa ka da Allah ya kosar da cikinshi.Muka ce Ibn Kasir yace yana daga cikin falalolin Mu’awiyah a cikin Al-Bidayah Wan Nihayah,sabanin abinda kake tsammani.Shine abinda muka ce taimakon Sahabi a fuskan Manzon Allah (sawa).Wato dole ya zama an warware mataki ko matsaya ko hukuncin Manzon Allah (sawa).
Rundinonin Sunnah ba zaka same su a gefen Manzon Allah (sawa) ba,ina nufin wa’yanda suke da’awan kare Sunnah saidai ka same su a dayan gefen(darful maqabil) don kare wanda Manzon Allah (sawa) yayi ma addu’a,kuma muka ce wannan itace jarabawan ‘yan shi’a.Jarawaban ‘yan shi’a itace kokarin tsayawa inda hukuncin Manzon Allah(sawa).
Wato shi Ibn Kasir sai ya kirga wannan addu’an daga cikn falalolin Mu’awiya saboda Mu’awiya bai da wata falala in banda wannan,za mu gani.Ibn Kasir a cikin Al-Bidayah Wan Nihayah yake cewa:
“Hikaka Mu’awiya ya amfana da wannan addu’an ta Manzon Allah (sawa) a duniyarshi da lahirarshi.To, amma  a cikin duniya-yanda  aka yi ya amfana da addu’an Manzon Allah cewa ka da Allah ya kosar dashi-domin shi Mu’awiya a lokacin da ya zama Ameer wato Sarki a Sham(Siriya ta yanzu) ya kasance yana ci sau bakwai a yini,ana zuwa mashi da gidauniya babba wadda a cikinta akwai nama mai yawa da kuma albasa mai yawan gaske,sai ya dinga ci daga wannan gidauniyyar.A cikin kowanne yini yana cin abinci da nama,sannan yana ci daga halawa mai yawan gaske a yini yana sha,sannan ana kawo mashi kayan marmari da abubuwa masu yawan gaske.
Kuma ya kasance ya kance wallahi ban koshi (wato ko mai ya ci bai koshi) saidai kawai in gaji da cin abinci amma ban koshi-ka ga wannan fadila ce in ji Ibn Kasir.Wannan kuma ni’ima ce kuma kowanne Sarki daman yana so a dinga kawo mashi abinci kala kala yana ci,to sai ya zama Mu’awiyah ya ni’amta da wannan ni’ima din,wato yana yin abinda sarakuna suke bugata.Ka ga shi yasa Annabi yayi mashi addu’a ya zama yana cin abinci da yawa.Wato ba addu’a bace “alaihi” addu’a ce “lahu” wato addu’a ce gare shi in ji Ibn Kasir.Wannan shine malkoya nassi,shine “tahrif”wato jirkita nassi daga inda aka ajiye shi daban da inda aka saukar dashi daban.Wannan ta amfane shi a duniya kenan”.
Amma a inda ya amfana da wannan addu’an a lahira zamu bari sai mun zo hadisin Muslim.Ya amfana da wannan addu’an inji Ibn Kasir,wannan yana da dangantaka ne kai tsaye da hadisin Muslim.In muka zo karanta hadisin Muslim sai mu dawo mu ji me Ibn Kasir yake nufi da cewa Mu’awiya ya amfana da wannan addu’an a lahira.288