14 Disamba 2016 - 10:04
Kimanin 'Yan Ta'adda 1500 Suka Mika Kansu  Ga Sojojin Syria

'Yan ta'adda 1500 ne suka mika kansu da makan da ke hannunsu a jiya ga rundunar sojin kasar Syria a yankin Kanakar da ke kudancin birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran kasar Syria na SANA ya bayar da rahoton cewa, 'yan ta'adda sun mika kansu ne domin samun afuwar da shugaba Bashar Assad ya yi duk wani mai dauke da makami, matukar ya tuba ya kuma mika kansa da makaminsa, sauran 'yan ta'adda da suka shigo daga kasashen ketare kuwa, su koma ta inda suka shigo wato Turkiya.

Hakan na faruwa ne  daiadi lokacin da sojojin Syria tare da kawayensu suka kammala murkushe 'yan ta'adda a birnin Aleppo, birni mafi girma a kasar ta Syria, kuma babbar cibiyar kasuwancin kasar.

Kasashen da ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Syria sun nuna takaicinsu matuka dangane da nasarar da sojojin Syria suka samu wajen kwace iko da birnin na Aleppo daga hannun 'yan ta'addan, inda suke kallon hakan a matsayin wata babbar nasara ga gwamnatocin Syria, Iran da kuma Rasha gami da kungiyar Hizbullah.288