2 Nuwamba 2016 - 18:07
Jagora: Sasantawa Da Amurka Ba Zai Magance Matsalolin Da Ake Fuskanta Ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar shiryawa da Amurka ba zai taba magance matsalolin da kasar Iran take fuskanta ba, don kuwa Amurkan ba ta yi watsi da kiyayyar da take nunawa al'ummar Iran ba.

Ayatullah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba a wata ganawa da dubun dubatan daliban makarantu na na Iran don tunawa da zagayowar ranar da daliban jami'oin Iran magoya bayan tafarkin marigayi Imam Khumaini (r.a) suka kame ofishin jakadancin Amurka a Tehran a shekarar 1979, inda ya ce Amurkawa da wasu mutane suna kokarin sanya wa mutanen Iran tunanin cewa sasantawa da Amurka zai magance matsalolin da Iran take fuskanta alhali lamarin ba haka ba ne.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa wannan tunani, na cewa idan muka sasanta da Amurka, za a magance dukkanin matsalolin da Iran take fuskanta, lalle tunani ne mai matukar hatsarin gaske.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ishara da irin kiyayya da makirce-makircen da Amurka ta kulla kuma take ci gaba da kulla wa al'ummar Iran tsawon sama da shekaru talatin din da suka gabata, don haka ya ja kunne dangane da masu tunanin cewa sasantawa da kuma sassautowa zai magance matsalolin da Iran take fuskanta a halin yanzu yana mai cewa koda wasa don kuwa Amurkawan har ya zuwa yanzu ba su daina irin wannan kiyayya da suke yi da al'ummar  ta Iran ba; duk dai da nufin dakile irin ci gaba da Jamhuriyar Musulunci da Iran da  kuma al'ummar kasar suke samu ba.

Ranar 13 ga watan Aban, wato 3 ga watan Nuwamba 1979 rana ce da gungun daliban jami'a magoya bayan marigayi Imam Khumaini (r.a) suka mamaye ofishin jakadancin Amurka wanda a lokacin ya zamanto wata sheka ta leken asiri da kulla makirci wa juyin juya halin Musulunci da jaririyar gwamnatin Musulunci ta Iran din da ba ta jima da kafuwa ba.288