A nan iran dai an raya daren jiya wato daren Ashoora don tunawa da halin da Imam Husain (a) jikan manzon All...(s) da kuma iyalan gidansa suka shiga a karbala kafin kissan gillar da sojojin Yazid Dan Mu'awiya suka yi masu a rana a irin ta yau a lokacin.
A nan Tehran dai an raya daren na Ashoora a duk fadin birnin, daga ciki har a gidan jagoran juyin juya halin Musulunci a Sayyeed Aliyun Khaminae. Ana saran a safiyar yaune a karanta tarihin yadda aka gudanar da yaki tsakanin dubban mayakan yazid dan mu'awiya da kuma sahabban Imam Husain(a) a karbala har zuwa bayan shahadarsu gaba daya.
Sannan miliyoyiyun masu makoki zasu zagaya kan titunan biranen kasar don bayyana alhininsu da wannan kisan, wanda shi ne masomin farkawar musulmi a duk tsawon tarihi.
A birnin beyroot na kasar Lebanon ma Sayyed Hassan Nasurullah shugaban kungiyar Hizbullah ya raya daren na Ashoora da jawabai masu muhimmanci kan sauye sayen da ke faruwa a yankin musamman kan yakin da saudia da kawayenta suke kaiwa a kan kasar Yeman. Da matsalolin yaki da ta'addanci a siria da Iraqi.288