Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa lauyoyin Jean Ping dan takarar shugabancin kasar da ya sha kayi da kuma na Ali Bongo shugaban kasar mai ci sun cimma matsaya kan sake kidayen kuri'u na mazabu dubu biyu da 579 a jiya Talata.
Bayan zaben shugabancin kasar ta Gabon,an samu tashin hankali , tun bayan da hukumar zabe ta sanar da shugaba Bongo a matsayin wanda ya lashen zaben.
Hukumar zaben dai ta sanar da cewa Shugaba Ali Bongo ne ya lashen zaben shugaban kasar da kashi 49,85%, yayin da abokin hamyarsa Jean Ping ya samu kashi 48,23%, duk da irin takadamar bayan zaben da aka sha, daga karshe madugun 'yan adawar ya amince da shiga kotu inda ya bukaci da a sake gidaya kuru'u a wasu Mazabun da shugaba Ali Bongo ya yi ikrarin cewa ya samu kashi 95% na yawan kuri'un da Al'umar yankin suka kada.288