Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera cewa, a sakamakon hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a zirin Gaza tun daga safiyar yau Lahadi, mutane 150 ne suka yi shahada, 69 daga cikinsu kuma sun kasance a birnin Gaza da kuma arewacin yankin.
A wannan hare-haren 'yan jarida 5 sukai shahada a yau a zirin Gaza
Inda Majiyar labaran Falasdinu ta bayar da rahoton shahadar wasu karin 'yan jarida 5 a hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a zirin Gaza tun da tsakar daren jiya.
Ƴan jaridar Abdurraahman Al-Abadilah, Aziz Al-Hajjar, Ahmed Al-Zinati, Khaled Abu Saif da Nour Qandil sune 'yan jarida 5 da suka yi shahada.
Sannan an tabbatar da shahadar "Zakariya Al-Sinwar", dan'uwan Yahya Al-Sinwar a Gaza
Dakta "Zakaria Sinwar" farfesa ne a tarihin zamani a jami'ar Musulunci ta Gaza ya yi shahada tare da 'ya'yansa uku a hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan tantunan 'yan gudun hijirar Falasdinu a sansanin Nuseirat a daren jiya.
Shi dan uwa ne ga shahidi Yahya Sinwar, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas.
Your Comment