16 Mayu 2025 - 14:14
Source: ABNA24
Miliyoyin Jama’a Ne Suka Fito Muzaharar Nuna Goyon Bayan Gaza A Kasar Yemen

Al'ummar kasar Yemen sun sake bayyana goyon bayansu ga al'ummar Gaza da ake zalunta inda suka fito kwansu da kwarkwatarsu kan titunan birnin Sa'ada a Yamen.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbaiti (as) - ABNA - ya habarta cewa: Tashar Al-Masirah a yau Juma’a ta ruwaito cewa, an gudanar da wani gagarumin taro mai farin jini a dandalin tsakiyar lardin Sa’ada domin nuna goyon baya ga Palastinu.

An gudanar da gangamin ne karkashin taken "Muna Tare da Gaza wajen fuskantar kisan kiyashi da yunwa," kuma dubban mazauna yankin ne suka halarci taron.

Rike da alluna da rera taken "Ba za mu bar Gaza ita kadai ba" da kuma "Yakin da aka yi alkawarin zai faru da jihadi yana ci gaba," mahalarta taron sun nuna bacin ransu kan ci gaba da hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ke ci gaba da kai wa zirin Gaza da kuma hana gudanar ayyukan jin kai a yankin.

Wannan yunkuri na jama'a yana faruwa ne yayin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza kuma kungiyoyin kasa da kasa sun yi gargadin afkuwar bala'in jin kai.

Al'ummar kasar Yemen musamman a lardin Sa'ada sun sha nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar Palastinawa ta hanyar gudanar da jerin gwano da ayyukan tallafi.

Har ila yau, an shirya cewa bayan sallar Juma'a, za a gudanar da wani tattaki na miliyoyin mutane a Sana’a babban birnin kasar Yemen, domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza da kuma gwagwarmayar Palasdinawa

Your Comment

You are replying to: .
captcha