16 Mayu 2025 - 14:55
Source: ABNA24
Ba Za A Taba Tsagaita Wuta A Gaza Ba / Trump Yazo Kasashen Larabawa Ne Don Kawar Da Bashin Dala Tiriliyan 42 Ne.

Qatar dai ta gamsar da Hamas cewa sakin Eidan zai kasance musanya ga tsagaita wuta, yarjejeniya, da shigar da kayan agaji cikin Gaza.

Jaridar Ra’ayul Youm ta buga wata Makala wanda Abdul Bari Atwan ya rubuta kamar haka:

Kafofin yada labarai sun sha bayyana ziyarar shugaban Amurka Donald Trump a yankin (Saudiyya, Qatar, da Hadaddiyar Daular Larabawa) a matsayin ''tafiya mai cike da tarihi'' a cikin ci gaba da yada jita-jita da yada labarai da ba a taba ganin irinsa ba".

Batu na farko game da cece-kucen da kafafen yada labarai suka ambata shi ne ziyarar Trump a Riyadh ba ita ce ta farko ba. Trump kuma ba shi ne shugaban Amurka na farko da ya ziyarci babban birnin Saudiyya ba. To mene ne buqatar duk wannan hayaniyar?

Batu na biyu kuma shi ne wuce gona da iri wajen bayyana "tsamarin dangantaka" da ke tsakanin Trump da babban abokinsa Benjamin Netanyahu, firaministan mulkin mallaka na Sahayoniya. Yayin da a kwanakin nan mun shaida sakin "Aidan Alexander," wani fursuna Ba'amurke wanda bashi da kimar siyasa ko soja. Kunga ina wannan "rikicin dangantaka" da suke fada tsakanin Trump da Netanyahu bisa hakika a cikin labarin?

Ba wai kawai alaka da dangantaka tsakanin su ba ta tsaya ba ne, kai harma tafiyar Trump nan gaba zuwa Tel Aviv ya kusan tabbata ne, domin shugabannin “Isra’ila” ne ke mulkin Amurka, ba wai akasin haka ba.

Trump dai ya ziyarci wannan yanki ne domin dakatar da wawure dukiyar kasa da tabarbarewar tattalin arzikin kasarsa gwargwadon iko. Bashin da ake bin Washington ya haura dala tiriliyan 42, kuma yankin Gulf na Farisa ne kawai zai iya baiwa Trump damar cimma wannan buri, ba abokansa na Turai ba!

A gefe guda kuma, "Isra'ila" tana karɓar biliyoyin daloli daga Amurka kuma ba ta taba mayar da su ba.

Bayyanar Cin Amanar Shugabannin Larabawa Na Baya-Bayan Nan.

Amurka ta karbo fursunanta (Aydan) ba tare da an biya diyya ba.

Qatar dai ta gamsar da Hamas cewa sakin Eidan zai kasance musanya ga tsagaita wuta, yarjejeniya, da shigar da kayan agaji cikin Gaza.

Maganar gaskiya kawai ita ce kasashen Larabawa da Turkiyya suna anfani da jinananmu suna kasha al'ummarmu don su samu kusanci gaTrump don haka suka mika masa wannan fursuna a matsayin kyauta. Alhali ana ta ci gaba da killacewa da ci gaba da kisan kiyashi ga al’ummarmu, yunwa ta na kara kamari, zalunci yana ci gaba, cin amana ta na ci gaba.

Ya kamata a lura da cewa, a yayin wannan musayar, Amurka ta sami damar samun bayanai kan inda wasu kwamandojin Falasdinawa suke, tare da bayar da su ga masu aiwatar da ta’addancin kisa wato yahudawan sahyuniya domin su kasha su.

Ba Za A Taba Tsagaita Wuta A Gaza Ba

Sakataren harkokin wajen Amurka Mark Rubio: Amincewar da Amurka ta yi da gangan na ci gaba da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa; Hanyar zaman lafiya ita ce kawar da Hamas!!!

Mun yi imanin cewa kawar da Hamas gaba daya zai haifar da zaman lafiya' Muna goyon bayan duk wani taimako da ya isa ga mutanen Gaza; Matukar Hamas ba za ta iya satar wannan taimako daga jama'a ba! Matukar dai kungiyar Hamas tana aiki, to ba za a samu zaman lafiya ba. Ƙarshen waɗannan rikice-rikice yana yiwuwa ne kawai tare da mika wuyar da Hamas zata aiwatar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha