Bari kuma mu dan fadi wasu kalmomi game da bahasin siyasar da ake ta tadawa a yankin da duniya cikin ‘yan kwanakin nan. Wasu daga cikin kalaman da shugaban Amurka ya yi a ziyarar da ya kai yankin ba su cancanci mayar da martani ko kadan ba akansu. Domin Matsayin jawabin ya ƙasƙanta wanda hakan ya zama abin kunya ga mai magana da kuma abin kunya ga al'ummar Amurka. Ba za mu yi Magana akansu ba. Amma ya kamata mu lura da jumla ɗaya ko biyu dangane da hakan.
Trump ya ce yana so ya yi amfani da mulki wajen wanzar da zaman lafiya; Karya ya ke. Domin shi da jami’an Amurka, gwamnatocin Amurka, sun yi amfani da karfinsu wajen aiwatar da kisan gilla a Gaza, wajen rura wutar yaki a duk inda za su iya, wajen tallafa wa ‘yan amshin shatan su; Sun yi amfani da wannan ikon. Yaushe ne su kai amfani da mulki wajen samar da zaman lafiya? Haka ne, ana iya amfani da iko wajen samar da zaman lafiya da tsaro; Wannan ne ma ya sa duk da bakincikin da makiyanmu suke yi, za mu kara karfin kanmu da karfin kasarmu a kullum da Allah Ya yarda. Amma su ba su yi wannan aikin ba; Sun yi amfani da karfin da suke da shi wajen bai wa gwamnatin sahyoniya bama-bamai masu dauke da tan goma don jefa wa yaran Gaza, asibitoci, gidajen mutane a Labanon, da duk inda za su iya. Wannan shi ne batu na farko.
Shugaban na Amurka yana ba wa wadannan kasashen Larabawa wani abin koyi wanda a nasa maganar yana nufin wadannan kasashe ba za su iya rayuwa ko da kwanaki goma ba tare da Amurka ba. Ya ce kamar haka: Ya ce da Amurka ba ta kasance ba, ba za su iya kulawa da kan su ba tsawon kwanaki goma ba. Amurka ce ke kulawa da su. Yanzu, a cikin salon mu'amalarta, da halayenta, da salon shawarwarinta, tana sake gabatar masu da ba su shawarar su bi wannan tsari tare tilasta masu, ta yadda ba za su iya rayuwa ba tare da Amurka ba. Wannan samfurin tsarin tabbas ya gaza bai cimma nasara ba. Bisa kokarin yunkurin al'ummomin yankin, dole ne Amurka ta bar wannan yankin kuma zata fice daga yankin. Ko shakka babu, a wannan yanki, tushen cin hanci da rashawa, yaki, da sabani, ita ce gwamnatin Sahayoniya. Dole ne kuma za a tumbuke gwamnatin Sahayoniya, wacce ke da hatsarin gaske da ta zamo cutar kansa a wannan yanki.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da wasu ka'idoji na musamman, da tsarin hadafofi na musamman, kuma duk da irin wadannan matsaloli da suka faru a kewaye da mu, ta dogara da wadannan ka'idoji da ciyar da kasa gaba. Iran ta yau ba Iran din shekaru talatin da suka gabata ba ce, shekaru arba'in da suka gabata, ko shekaru hamsin da suka gabata. A yau bisa nasarar Ubangiji, da yardar Ubangiji, duk da kiyayyar da makiya suke yi, kuma duk da irin kyamar da wasu suke yi, Iran ta ci gaba, kuma in sha Allahu za ta ci gaba, kuma kowa zai ga haka. Matasanmu za su ga haka a mafi kyawun yanayi kuma in Allah ya yarda kowa zai ba da hadin kai wajen gina Iran Musulunci da kowa yake so.
Your Comment