1 Yuni 2016 - 14:37
'Yan Bindigar Niger-Delta Sun Sake Tarwatsa Bututun Mai A Yau Laraba

'Yan bindiga na kungiyar Avengers a yankin Niger-Delta sun sake kaddamar da wasu hare-hare kan bututun mai na kammafanin Chevron a kusa da Warri.

Kamfanin dillanicn labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, kungiyar ta Niger Delta Avengers ta sanar a cikin wani bayani cewa ita ce take da alhakin kaddamar da wanann hari.

A cikin wannan mako ne shugaban tarayyar Najeriya ya sanar da cewa za a dauki matakin murkushe 'yan bindigar an Niger Delta da karfin tuwo.

Hare-haren dai sun jawo ma Nijeriya matsaloli masu yawa, musamamn ta fuskar haka da kuma fitar da danyen man fetur, inda a halin yanzu da kyar Najeriya ke iya fitar da ganga miliyan 1.4, maimakon miliyan 2.5 da take fitar a lokutan baya.288