Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna- wanda ya lakanto daga IRINN- yace wata mota ce makare da Bom ta fashe inda tai sanadiyar mutuwar mutane 12 kuma fiye da 30 suka jikkata.
Wasu na gani kai harin na da alaka da taimako da mutanen garin Basara ke yima sojin kwamnati wajan yakar 'yan kungiyar ta'adda na Da'ish wadan da suka addabi mutanen kasar.
A gefe daya sojin Iraki tare da hadin gwiwar sojin sa kai na cigaba da samun nasara a yankunan Al'anbar a fafatawar da suke da 'yan ta'adda.ABNA