25 Disamba 2014 - 11:21
Ganawar shugaban majalisar jamhuriyar musulunci ta Iran da Firaministan Iranki.

Shugaban majalisar jamhuriyar musulunci ta Iran a yayin ganawa da firaministan Iranki yace: kasashen hadin kwiwa na Amruka wajan yaki da yan ta'adda na Da'ish a syria da Iraki kawai suna wasa da hankullan jama'a ne.

Taskar labarai ta Ahlulbai {a.s}-Abna-ta rawaito-dokta Ali larijani ayayin ziyararsa ta kasashen yankin wanda ahalin yanzu yake Iraki, lokacin da yake kanawa da haidar Abad firaministan Iraki yace; halin kakanikayi da yankin ya fada abune mai matukar muhimmanci kuma za'a iya warware shi ta hanyar hadin kan kasashen yankin.

Shugaban majalisar yayi nuni da cewa kasashen hadin kwiwa wadanda Amurka ke jagoranta domin yaki da kungiyar Da'ish suna wasane da hankulan Al'umma ba wai da gaske suke ba.

Ayayin ganawar Haidar Abad ya nuna farin cikinsa da kuma godiya ga jamhuriyar musulunci ta Iran wadda take taimakama kasar tashi cikin dadi da tsanani, da yake nuni da halin da ake ciki Haidar Abad yace;  ni shaidane akan cewa Iran tashiga yakin ne da kyakyawar niya kuma mutanen Iraki ba zasu taba mantawa da irin wannan sadaukarwa ba.

Firaministan Iraki yaci gaba da cewa; kasashen biyu Iran da Iraki ya kamata su zamo cikin sahu daya a siyasa da tattalin Arziki domin kuwa suna da bukatar junansu.ABNA