13 Nuwamba 2014 - 15:24
Kungiyar Likitoci Na Kasa Da kasa Ta Ce Ana Shirin Fara Gudanar Da Gwajin Magungunan Ebola

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta sanar cewa za a fara gudanar da wani gwajin wasu maguguna domin yaki da kwayoyin cutar Ebola, da nufin kawo karshen wannan cuta musamman a yankunan da ta fi tsananta a yammacin nahiyar Afirka.

A cikin bayanin da kungiyar likitocin ta kasa da kasa ta fitar yau, ta bayyana cewa an kammala dukkanin shrye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan gwaji, wanda kuma za a gudanar da shi ne matakai 3, tare da hadin gwiwa da wasu manyan cibiyoyin na kiwo lafiya a kasashen Birtaniya da Faransa, tare da sanya idon hukumar lafiya ta duniya WHO.

 

Bayanin ya ce sakamakon gwajin a matakai 3 shi ne zai bayar da tabbaci kan inganci ko rashin hakandangane da sabbin magungunan na cutar Ebola. Sabon rahoton hukumar lafiya ta duniya dai ya yi nui da cewa mutane 5160 ne suka rasa rayukansu,a cikin mutane 14,098 da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayoyin cutar. ABNA