14 Oktoba 2014 - 15:18
Kungiyar Yaki Don Dawo Da Yan Matan Chibok Zata Gudanar Da Zanga Zanga

Kungiyar nan mai Fafutukan dawo da yan mata yan makarantar garin Chibok a arewa maso gabacin tarayyar Nigeria wadanda Boko Haram ta sashe wacce kuma aka fi saninta da “Bring Back Our Girls campaign” zata gudanar da wani machi ko jerin gwanano zuwa ofishin shugaban kasa a Abuja a yau Talata don juyayin cika wattani 6 cur da sace yan matan.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce a rana irin ta yau ce 14-Afrilu na wannan shekarar, mayakan Boko Haram suka farwa wata makarantar yan mata a garin Chibok na jihar Bornon, a arewa maso gabancin kasar a cikin dare, inda suka sace yan mata yan makaranta 276 wadanda suke da shekarun haihuwa tsakanin 12 zuwa 17, suka kuma kora su, suka shiga daji da su.

Daga bayan da  wasu yan mata 57  daga cikinsu sun sami damar tserewa, daga hannun Boko Haram, amma har yanzun akwai yan mata kimani 219 wadanda har yanzun ba’asan makomarsu ba.

Zanga zangar ta yau dai, zata kai yayan wannan kungiyar ga ofishin shugabankasa Dr Goodkuck Jonathan don kara takura masa kan wajibcin dawo da yan matan ga hannun iyayensu.

Enoch Mark, daya daga cikin dangin yan matan ya fadawa AFP cewa ba za su dabe kauna daga dawowar yan matan ba, musamman bayan da aka gano daya daga cikinsu a cikin yan kwanakin da suka gabata. ABNA