Sa’ib Uraikat babban jami’in Palasdinawa da ke jagorantar zaman tattaunawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana cewar firan ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benyamin Netanyahu a kullum yana kokarin mai da rikicin siyasar yankin gabas ta tsakiya a matsayin rikicin addini. Uraikat ya kara da cewar Netanyahu ya dage kan batun kiran haramtacciyar kasar Isra’ila da sunan daular addini ta yahudawa kuma yana ci gaba da aiwatar da ayyukan ta’addanci tare da goyon bayan tsagerun yahudawan sahayoniyya da suke aiwatar da kisan gilla kan Palasdinawa da kona masallatai da majami’un kiristoci, kamar yadda Abubakar Bagadadi ke da’awar kafa daular addini tare da aiwatar da kashe-kashen gilla kan jama’a da rusa wajajen ibadu.
Har ila yau Sa’ib Uraikat ya fayyace cewa; Netanyahu yana kokarin tsoratar da duniya kan kungiyar ta’addanci ta Da’ish alhalin ayyukansa ba su da bambanci da na kungiyar ta Da’ish. Wannan furuci na Sa’ib Uraikat ta zo ne a matsayin mai da martani kan furuci Netanyahu da ya siffanta kungiyar Hamas da kungiyar ta’addanci ta Da’ish a jawabinsa a gaban zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin da ta gabata. ABNA