16 Satumba 2014 - 08:58
Iran:Jagora Ya Ce Ba ZamuHada Kai Ba Da Wadanda Hanunsu Ya Cudu Da Jinin Al'umma Wajen Yaki Da 'Yan Ta'adda

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran ya ce bayanan magaban Amurka na kafa wata kungiyar wacce za ta yaki kungiyar ‘yan ta’addar da’esh a kasashen iraki da Siriya ba da gaske ne ba. A yayin da aka sako shi daga Asibiti Ayyatull.

Ali Khamnayi ya bayyana cewa a maganganun magabatan Amurka za a fahimci cewa karya ce suke musaman ma dangane da kiran jumhoriyyar musulinci ta Iran. A kwanakin baya, jakadan kasar Amurka a iraki ya nemi jikadanmu na iraki da su tattauna domin yakar kungiyar Da’esh, muka ki amincewa saboda ba zamu hada kai ba da wadanda hanunsu ya tsudu da zibar da jinin bayin Allah da kuma aikata munanan aiyuka a duniya don haka cewa ba za a kayyaci Iran ba a wannan mumunan abu, abin alfahari ne a garemu.

 

Jagora ya kara da cewa firicin da saktaren harakokin wajen Amurka yayi na cewa ba za a gayyaci jumhoriyyar musulinci ta iran ba wajen yaki da kungiyar ‘yan ta’addar ISIS a kasar Iraki karye ce, domin sun tuntuba ba su sami amincewa ba, kuma nasarar da Ake samu yanzu haka a kasar Iraki aiyuka ‘yan kasar ba Amurka ba. ABNA