8 Yuli 2014 - 09:47
Jagora: Babu Wata Kasa Da Take Da Karfin Halin Kaddamar Da Harin Soji Kan Kasar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa; Babu wata kasa da take da karfin halin da zata iya kaddamar da harin soji kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran

A jawabinsa ga taron manyan jami’an gwamnatin Iran a jiya Litinin; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i ya bayyana cewa; Akwai masu cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana son kaddamar da harin soji kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran amma gwamnatin Amurka tana adawa da hakan; Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya fayyace cewa; A fili yake dalilin gwamnatin Amurka na nuna rashin amincewa da duk wani harin soji kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran shi ne babu wani tasirin da harin zai yi kan kasar Iran kuma babu wani amfani da maharan zasu samu, don haka babu abin da ya rage ga makiya sai ci gaba da kakaba takunkumi da barazana kan kasar ta Iran da kuma kokarin ganin sun rikita duk wani lissafin mahukuntan kasar.

Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya jaddada amincewarsa ga tawagar kasar Iran da take gudanar da zaman tattaunawa da bangaren kasashen yammacin Turai kan shirin Iran na makamashin nukiliya; yana mai cewa; Tawagar ba zata taba amincewa a tauyaye hakkin al’ummar Iran na mallakar cikakken fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya ba.ABNA