Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Bankin Raya Afirka ya amince da bai wa Morocco rance na Yuro miliyan 205 (kimanin dala miliyan 234) da nufin tallafawa faɗaɗa hanyar jirgin kasa mai saurin gaske da kuma sabunta ababen more rayuwa na jirgin kasa, yana mai cewa tallafin yana da nufin "ƙarfafa ƙarfin ɗaukar kaya da aiki a kan hanyar Kenitra-Marrakech, wadda ke ɗaukar kaso mai yawa na zirga-zirgar fasinjoji da kayayyaki a Morocco."
Wannan rance yana cikin babban shirin Morocco na zuba jari a hanyoyin jirgin kasa, inda Rabat ke shirin zuba kusan dala biliyan 10 don faɗaɗa hanyoyin jiragen kasa tsakanin garuruwa da na birane, ciki har da gina sabuwar hanyar jirgin kasa mai saurin gaske da za ta kai Marrakish, kafin Morocco ta karbi bakuncin wani sashe na gasar cin kofin duniya ta 2030 tare da Spain da Portugal.
Sabuwar hanyar jirgin kasa mai saurin gaske za ta tashi daga Kenitra da ke gabar Tekun Atlantika zuwa kudancin Maracco, mai tsawon kilomita 430, ta ratsa babban birnin Rabat da birnin Casablanca, wanda zai ƙarfafa haɗin kai tsakanin manyan cibiyoyin tattalin arziki da yawon bude ido a ƙasar.
Morocco a watan Afrilu 2025 ta fara babban shirin faɗaɗa hanyoyin jirgin kasa wanda darajarsa ta kai kusan dirham biliyan 96, wanda ya haɗa da dangana hanyar jirgin kasa mai saurin gaske zuwa Marrakish, da siyan sabbin jiragen kasa, da faɗaɗa hanyoyin jirgin kasa don hidimar ƙarin garuruwa nan da 2040.
Waɗannan zuba jari suna cikin shirye-shiryen Morocco don karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2030, amma suna da manyan manufofin tattalin arziki, waɗanda suka shafi inganta haɗin kai tsakanin manyan garuruwa, rage lokacin tafiya, rage matsin lamba a kan tituna, da tallafawa sassan yawon bude ido, ayyuka da masana'antu.
Hanyar Kenitra-Marrakish tana da muhimmanci na musamman, domin tana haɗa arewa da tsakiyar ƙasar da yankin kudu na yawon bude ido, kuma tana ratsa Rabat da Casablanca, waɗanda suke daga cikin garuruwa mafi yawan zirga-zirgar kasuwanci da tafiya ta yau da kullun da haɗayyar aiki da tashoshin ruwa da filayen jiragen sama.
..................
Your Comment