Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: An fara taron girmamawa na kwamitocin waje ga jagora shahidin juyin juya halin Musulunci, Mai girma Ayatullahil-Uzma Imam Sayyid Ali Khamene'i (Allah ya yi masa rahamarsa) a filin sallah na Imam Khomeini a Tehran.
A wannan taron, wasu gungun shugabannin siyasa, malamai, masana da kuma shugabannin addinai daga kasashe daban-daban na duniya, ta hanyar halarta kusa da gawar shahidin jagoran juyin juya hali, sun karanta suratul Fatiha da kuma nuna juyayi, sun kuma yi gaisuwar girmama tunawa da gwagwarmayar da ya yi don kare al'ummar Musulunci da kuma goyon bayan al'ummomin da ake zalunta.
Karfe 11:01 Na Safe | Halartar Da Shigowar Wata Tawaga Daga Mata Daliban Addini Da Masu Fafutuka A Fagen Kasa Da Kasa Don Yin Girmamawa Ga Gawar Jagora Shahidin Juyin Juya Halin Musulunci.
Karfe 10:46 | Shigowa Da Bankwana Da Iyalan Shahid Sayyid Hassan Nasrallah Da Imad Mughniyah Da Iyalan Kwamandojin Shahidai Na Hizbullah Suka Gudanar Ga Jagora Shahidin Juyin Juya Hali.
Karfe 10:39 | Shugowa Da Girmamawar Tawaga Daga Gidan Jagora Mai Girma Shahidin Juyin Juya Hali Ga Gawar Imam Shahidi.
Karfe 10:34 | Girmamawar Wata Tawaga Daga Malaman Falasdinu Ga Gawar Jagora Shahidin Juyin Juya Halin Musulunci.
Karfe 10:30 | Girmamawar Shugabannin Hindu, Shi'ar Thailand Da Jamus Ga Gawar Shugaba Shahidin Al'umma.
Karfe 10:25 | Shigowar Tawaga Daga Malamai Da Musulman Rasha Don Yin Girmamawa Ga Shugaba Shahidin Al'umma.
Karfe 10:20 | Shigowar Tawaga Daga Georgia Don Yin Girmamawa Ga Jagora Mujahidi Shahidin Iran.
Karfe 10:11 | Girmamawar Wakilan Majalisa Da Jam'iyyar Republican Ta Bulgaria Ga Gawar Imam Shahidi.
Your Comment