26 Yuni 2026 - 22:14
Source: ABNA24
Tucker Carlson: Shekaru Da Yawa Na Yi Kuskure Game Da Musulunci

Fitaccen mai watsa labarai mai ra'ayin mazan jiya a Amurka, a cikin wata sabuwar hira ya yi ikrarin cewa tunaninsa na baya game da Musulmai ba daidai ba ne.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: "Tucker Carlson," Manazarcin siyasa mai ra'ayin mazan jiya na Amurka, ya tabbatar da cewa matsayinsa na baya game da Musulunci da Musulmai kuskure ne. Wani sabon canji a cikin tunaninsa da siyasarsa wanda ya faru ne bayan ya raba riga da "Donald Trump" shugaban Amurka, da kuma ƙara sukar sa ga gwamnatin yahudawa. Batun da mujallar Newsweek ta yi nazari a kai a cikin wani rahoto.

Carlson a cikin hira da gidan talabijin na Sky News ya ce: Shekaru da yawa ina maimaitawa a shirye-shiryena na talabijin cewa matsalar ita ce Musulunci, kuma matsalar ita ce Musulmai, duk suna so su kashe mu. Ya kara da cewa: Na kasance cikin tashin hankali kuma na gaskata hakan. Yanzu na san cewa wannan ba gaskiya ba ne, kuma babu ɗaya daga cikin waɗannan maganganun da ke da gaskiya, amma a wancen lokacin na yi imani da su.

Wannan canjin matsayi bai tsaya ga Musulunci kawai ba, har ma ra'ayinsa game da gwamnatin yahudawa ya sami canji. Carlson game da wannan gwamnatin ya ce: Isra'ilar da na ziyarta shekaru da dama da suka gabata, ba ta yi kama da Isra'ilar yau ba. Isra'ila ta canza gaba daya, kuma ina baƙin cikin hakan.

Canje-canjen A Siyasar Carlson

A rubutun Newsweek, waɗannan maganganun sabon abu ne a cikin jerin canje-canjen siyasar Tucker Carlson a shekara ta 2026. Canje-canjen da suka faru bayan ya sanar da ƙare goyon bayansa ga Trump, da neman gafara game da batar da Amurkawa a goyon bayan da ya yi wa Trump a baya, da kuma sanar da rabuwa da jam'iyyar Republican.

Wannan rahoto ya yi nuni da cewa tarihin Carlson ya ƙunshi maganganu da yawa waɗanda masu suka ke ɗauka a matsayin masu adawa da Musulunci. A lokacin aikinsa a gidan talabijin na Fox News, ya gayyaci "Ihan Hursi Ali" mai fafutukar siyasa, ya soki dangantakar gwamnatin Joe Biden da Musulman Amurka, kuma ya kare yunkurin Trump na hana tafiya daga wasu kasashe, ko da yake ya yi iƙirarin cewa wannan yunkurin ba ya nufin iya Musulmai ba ne.

A cikin shekarun da suka gabata, wasu ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama, ciki har da Majalisar Dangantakar Musulunci da Amurka (CAIR), sun buƙaci a kori Tucker Carlson, kuma sun zarge shi da yada ra'ayoyin adawa da Musulunci, adawa da bakin haure, da kuma daidaita da ra'ayin fifikon launin fata.

Amma salon Carlson ya canza daga ƙarshen shekara ta 2025. Ya kira hare-haren da ake kai wa Musulmin Amurka a matsayin abin ƙyama, kuma ya ce tsoron Musulunci yana ƙaruwa ne daga gwamnatin yahudawa da magoya bayanta a Amurka.

A gefe guda, ƙaruwar sukar da Tucker Carlson ke yi wa gwamnatin yahudawa ya sa wasu su zarge shi da kyamar Yahudawa, zargi da Carlson ya musanta sosai. Newsweek ta rubuta cewa Ƙungiyar Yaƙi da Cin Zarafi (ADL), ta zarge shi da yada makircin ƙarya na kyamar Yahudawa, musamman bayan ya karbi bakuncin "Nick Fuentes" mai fafutukar kishin fararen fata wanda ya musanta kisan kiyashi na Holocaust.

Carlson ya mayar da martani cewa matsayinsa game da gwamnatin yahudawa, ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilar Yahudawa ba, a'a, yana da alaƙa da manufofin wannan gwamnati wanda a cewarsa yana cutar da bukatun Amurka.

Canji A Ra'ayin Jama'ar Amurka

Wannan rahoto, ya ɗauki canjin matsayin Carlson a matsayin wani bangare na canje-canje masu faɗi a ra'ayin jama'ar Amurka. Dangane da ma'auni na ƙasa na kyamar Musulunci, adadin yarda da ra'ayoyin da ba su dace ba game da Musulmai a Amurka ya ƙaru tsakanin shekarun 2022 zuwa 2025. Duk da haka, rarrabuwar kawuna na jam'iyyu har yanzu a bayyane take, ta yadda kashi 82% na 'yan Democrat na Amurka suna da kyakkyawan ra'ayi game da Musulmai, yayin da wannan adadi a tsakanin 'yan Republican ke da kashi 43%.

A lokaci guda, goyon bayan jama'a ga gwamnatin yahudawa ma ya ragu sosai. Dangane da binciken Cibiyar Bincike ta Pew a watan Maris na 2026, kashi 60% na Amurkawa suna da mummunan ra'ayi game da gwamnatin yahudawa.

Haka kuma bayanan Cibiyar Gallup sun nuna cewa a karon farko tun daga shekara ta 2001, adadin jin tausayin Amurkawa ga Yahudawa bai fi jin tausayinsu ga Falasdinawa ba. Alamar da ke iya nuna canji mai muhimmanci a yanayin ra'ayin jama'ar Amurka.

..................................

Your Comment

You are replying to: .
captcha