Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa waɗannan fashe-fashe sun samo asali ne daga hare-haren sama da Isra'ila ta kai a yammacin Gaza.
A na ta ɓangaren Ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu (Hamas), a cikin wata sanarwa, ta bayyana cewa Isra'ila, ta hanyar amfani da siyasar killacewa kakaba yunwa, da kai hari ga yara da fararen hula marasa tsaro, tana ci gaba da kisan kare dangi a Gaza.
Gwagwarmayar Musulunci ta Falasdinu ta nanata cewa, na'urar kisan kare dangi ta mamaya na ci gaba da aikata munanan laifuka a kan mazauna Gaza.
..........
Your Comment