26 Yuni 2026 - 15:55
Source: ABNA24
An Gudanar Da Muzaharar Ashura Na A Da’irar Katsina Najeriya + Hotuna

Da safiyar ranar Juma'a 11 ga watan Al-Muharrama, 1448, dai-dai da 26/06/2026 ne ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Da’irar Katsina, suka bi sahun sauran muminai na faɗin duniya baki daya, mabiya mazhabar Ahlulbaiti (S) wajan nuna alhini da juyayi, na kisan jikan Annabi Muhamamd, Imamul Hussain (A.S).

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Muzaharar na ci gaba da gudana yanzu haka lami lafiya, inda ’yan’uwa Maza da mata sanyen da baƙaƙen kaya, ke rera waƙoƙin juyayi da kuma ɗaga totoci masu rubutun “Ya Hussain” ko “Labbaika Ya Hussain” ...

A gaban Muzaharar, tsakiya da kuma karshenta Harisawa ne masu kula da tsari, nizami, sahu, da kuma ƙa'idar hanya, inda suke kula da ababen hawa da basu hanya domin wucewa ba tare da an samu cinkoso ko haɗari ba.

Ga wasu hotuna da aka ɗauka a yanzu haka:

لا يوم كيومك يا أبا عبد الله...

26Jun2026.

Your Comment

You are replying to: .
captcha