14 Yuni 2026 - 10:44
Source: ABNA24
Kwamandan Hedkwatar Khatamul-Anbiya (S.A.W) Ya Bayyana Ingancin Yanayin Kayan Tsaron Saman Iran

Birgediya Janar "Ali Reza Elhami" a cikin bayanin da ya yi a yau Lahadi ya yi bayanin ci gaban shirye-shiryen wannan runduna bayan tsagaita wuta a "Kallafaffen Yaƙi na Uku" (Yakin Ramadan), yana mai cewa: A yau, a cikin rundunar tsaron sama ta sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, duk abin da muke da shi na kayan aiki, tsare-tsare, dabarun yaƙi, cibiyoyin bayar da umarni da sarrafawa, abubuwan more rayuwa na sadarwa da sassan leken asiri, na Iran ne gaba ɗaya suna cikin inganci.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Kwamandan Hedkwatar Tsaron sama ta Hadin Gwiwa ta Khatamal-Anbiya (S.A.W) a Iran ya tabbatar da cikakken wadatar da kai da kayayyaki na tsaron saman ƙasar, yana mai cewa: Dukkan kayan aiki da tsare-tsare da cibiyoyin bayar umarni da sarrafawa da abubuwan more rayuwa na sadarwa da muke da su, an kera su ne bisa ilimin Iran 100% kuma a hannun masana ƙasar masu aminci.

Birgediya Janar "Ali Reza Elhami" a cikin bayanin da ya yi a yau Lahadi ya yi bayanin ci gaban shirye-shiryen wannan runduna bayan tsagaita wuta a "Kallafaffen Yaƙi na Uku" (Yakin Ramadan), yana mai cewa: A yau, a cikin rundunar tsaron sama ta sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, duk abin da muke da shi na kayan aiki, tsare-tsare, dabarun yaƙi, cibiyoyin bayar da umarni da sarrafawa, abubuwan more rayuwa na sadarwa da sassan leken asiri, na Iran ne gaba ɗaya suna cikin inganci.

Birgediya Janar Elhami ya tabbatar da cewa an sami waɗannan nasarorin ne bisa dogaro da ilimin gida 100% da kuma amfani da ƙarfin maza da masana na Iran din musulunci, ya kara da cewa: Ana iya samun wasu matsaloli ko raunin, amma masana da ƙwararrun tsaron sama na sojojin, tare da haɗin gwiwa ta kud-da-kud da ci gaba da cibiyoyin kimiyya da bincike na ƙasar, suna yin iyakacin ƙoƙarinsu don warware su.

Kwamandan Hedkwatar Tsaron sama ta "Khatamul-Anbiya" (S.A.W) ya yi nuni ga matakan da aka ɗauka don sake gina ƙarfin tsaron ƙasar, ya jaddada cewa: Duk ƙoƙarinmu yana kan cewa mu samar da kayan aiki da sabunta tsare-tsare da kayan aikin da suka dace saboda da barazanar da ake ciki a yanzu, da kuma maye gurbin kayan aikin da makiya masu laifi suka lalata a lokacin " Kallafaffen Yaƙi na Uku" cikin sauri.

Birgediya Janar Elhami ya ɗauki sirrin sabbin abubuwa na rundunar tsaron sama a matsayin dogaro da ƙarfin cikin gida, yana mai bayyana cewa: Lokacin da dukkan kayan aikin na gida ne, haɓaka su da sabunta su gaba ɗaya yana hannunmu, kuma muna sabunta kayan aikin bisa ga buƙatu; don haka, samar da su da yawa shi ma zai kasance a hannunmu, kuma a gaskiya ba mu buƙatar wani daga waje.

A ƙarshe, kwamandan rundunar tsaron sama ta sojojin ya yi godiya ga kamfanonin ilimi, ya jaddada cewa: A yau, duk ƙoƙarinmu yana kan sabunta kayan aikinmu daidai da barazanar da kuma kai su ga samar da su da yawa, tare da taimakon cibiyoyin kimiyya da bincike.

……………………………

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha