31 Mayu 2026 - 18:40
Source: ABNA24
Hizbullah Ta Kai Harin Rokoki Kan Rukunin Soji Na Isra'ila A Haifa

Hizbullah ta bayyana cewa mayakan gwagwarmayar Musulunci sun kai hari da rokoki kan rukunin sojin Isra’ila a Haifa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Hizbullah ta Lebanon ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa mayakan gwagwarmayar Musulunci a yau Lahadi sun yi ruwan rokoki kan rukunin soji na Sahayoniyya a garin "Al-Kiriyot".

A cikin sanarwar sun ce: "Domin kare Lebanon da al'ummarta, kuma a matsayin martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta daga bangaren Sahayoniya da cin zarafin da ta ke yi wa kauyukan kudancin Lebanon wanda ya haifar da shahada da raunata wasu fararen hula, mayakan gwagwarmayar  Musulunci a yau Lahadi, da ƙarfe 12:30, a ranar 31-05-2026, sun kai hari da rokoki kan rukunin soji na Sahayoniyya a garin 'Al-Kiriyot' da ke arewacin garin Haifa da aka mamaye."

Hizbullah ta Lebanon ta kuma bayyana cewa mayakan gwagwarmayar Musulunci a yau Lahadi, sun kai hari kan sojojin Sahayoniyya a kewayen yankin "Al-Sharqiyya" a garin "Yahmar Al-Shqif" da jirgin mara matuki a "Ababil".

Hizbullah ta nanata cewa wadannan hare-hare suna cikin tsarin kare Lebanon da al'ummarta, kuma a matsayin martani ga cin zarafin tsarin Sahayoniyya a kan kauyuka, ruguza gidaje, da shahada da raunata wasu fararen hula a kudancin Lebanon.

………………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha