24 Mayu 2026 - 08:06
Source: ABNA24
Daftarin Yarjejeniyar Iran Da Amurka Zai Kawo Ƙarshen Yaƙi A Dukkan Fagagen Daga

Jaridar New York Times a bayan sanarwar da shugaban ƙasar Amurka ya yi game da shirya yarjejeniya tsakanin Tehran da Washington da ake jiran kammalawa, ta yi iƙirarin cewa: Daftarin yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka zai haifar da kawo ƙarshen yaƙi a dukkan faɗin fagen yaki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bait (AS) - ABNA - ya ruwaito cewa: Jaridar Amurka New York Times a bayan sanarwar da Donald Trump shugaban ƙasar Amurka ya yi game da shirya yarjejeniya tsakanin Tehran da Washington da ake jiran kammalawa, ta yi iƙirarin cewa: Daftarin yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka zai haifar da kawo ƙarshen yaƙi a dukkan fagagen da ake arangama har da mashigar Hormuz.

Jaridar New York Times da yammacin ranar Asabar, ta nakalto daga wasu waɗanda ta kira "jami'an Iran guda uku", ta yi iƙirarin cewa: Daftarin yarjejeniyar da ake nazari a kai, zai haifar da kawo ƙarshen rigingimu a dukkan faɗin daga, kuma yana mai da hankali kan sake buɗe mashigar Hurmuz, gami da ɗage killacewar teku da Amurka ke yi.

Wannan kafar yaɗa labarai ta ƙara da cewa: Wannan yarjejeniya za ta ƙunshi 'yantar da dala biliyan 25 daga kadarorin Iran da aka killace a wajen ƙasar.

Wannan kafar yaɗa labarai ta Amurka ta yi iƙirarin cewa: Batutuwan nukiliya waɗanda suka kasance ɗaya daga cikin manyan wuraren sabani a tattaunawar, za a yi tattaunawa a kansu cikin kwanaki 30 zuwa 60 masu zuwa.

Jaridar New York Times ta yi iƙirarin cewa: Wannan yarjejeniya kuma za ta ba da cikakken 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hurmuz, kuma ba za a sanya wani harajin kuɗi don wucewar jiragen ruwa ba.

Jaridar New York Times ta yi iƙirarin cewa: Ba a sani ba ko shawarar jami'an Iran ita ce abin da Trump ya yi nuni da shi a rubutunsa a shafukan sada zumunta ko kuwa a'a.

Wannan kafar yaɗa labarai ta Amurka ta yi iƙirarin cewa: Masu sasanci na Pakistan da Qatar ne suka sauƙaƙe daftarin yarjejeniyar.

Abin lura shi ne, Donald Trump, shugaban ƙasar Amurka da yammacin ranar Asabar bisa ga agogon gida, 23 ga watan Mayu, 2026 ya yi iƙirarin cewa: An shirya yarjejeniya tsakanin kasar Amurka da Iran, kuma tana kan kammalawa. Ana ci gaba da nazarin fannoni da cikakkun bayanai na ƙarshe na yarjejeniyar, kuma ba da jimawa ba za a sanar da ita.

Trump a shafinsa na sada zumunta na Truth Social ya ce: "Ina cikin ɗakin Oval na Fadar White House, inda a yanzun na yi tattaunawa mai kyau da Muhammad bin Salman Al Saud na Saudi Arabiya, Muhammad bin Zayed Al Nahyan na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Amir Tamim bin Hamad bin Khalifa Al Thani, Firayim Minista Muhammad bin Abdulrahman bin Jassim bin Jabir Al Thani, da Minista Ali Al Thawadi na Qatar, Janar Asim Munir Ahmad Shah na Pakistan, Rajab Dayyib Erdogan shugaban ƙasar Turkiyya, Abdel Fattah El-Sisi shugaban ƙasar Masar, Sarki Abdullah na biyu na Jordan, da Sarki Hamad bin Isa Al Khalifa na Bahrain".

Ya ƙara da cewa: Waɗannan tattaunawar game da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da duk abubuwan da suka shafi yarjejeniyar fahimtar juna game da zaman lafiya ne. Yarjejeniya ce da aka kusan gama tattaunawa a kai, wacce za ta dogara ne akan kammalawa tsakanin kasar Amurka, Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sauran kasashen da aka ambata. Shugaban ƙasar Amurka ya ƙara da cewa: A wani bangare na daban, na yi tattaunawa da Bibi Netanyahu Firayim Ministan Isra'ila, wacce ita ma ta yi kyau sosai.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha