22 Mayu 2026 - 21:40
Source: ABNA24
Jiragen Hizbullah Sun Gurgunta Kashi 80 Cikin 100 Na Ƙarfin Sojojin Isra'ila A Kudancin Lebanon.

Hizbullah ta kai hari kan na’urar kariya "Kubbar Ƙarfe" a sansanin Isra’ila na Branit a arewacin yankunan da aka mamaye da jiragen marasa matuki na Ababil. Sannan ta danawa Sojojin Isra’la na musamman tarko mai tsanani.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Bisa ga abin da jaridar Ma'ariv ta buga na rahoton wani manazarcin soji "Alon Ben David" cewa: Wani gungun dakarun Isra’ila da ya ƙunshi "rukuni biyu na sojoji na musamman na Isra'ila " yayin da suke gudanar da wani aiki a yankin kogin Litani a kudancin Lebanon, sun fuskanci fashewar Bam da aka riga aka shiryata tun kafin su karasa.

Mayakan Hizbullah waɗanda suke lura da motsin wannan tawagar daga kusa, sun yi nazarin hanyar tafiyarsu da kyau. Sannan a lokacin da ya dace, bam ɗin da aka dasa a hanyar sojojin Isra'ila ya tashi, wanda sojoji huɗu suka ji rauni a wannan lamarin.

Wannan aiki, ta fuskar hanyar aiwatarwa, yana da kama da tsarin yaƙin da Hizbullah da su kan yi a kan sojojin Isra'ila a lokacin mamayar yankin tsaro na kudancin Lebanon a shekarun 1985 zuwa 2000.

…………………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha