22 Mayu 2026 - 21:27
Source: ABNA24
Asim Munir Ya Isa Tehran Domin Bibiyar Batun Tattaunawar Iran Da Amurka

Kwamandan sojojin Pakistan da yammacin ranar Juma'a, a cikin shirin yin sulhu tsakanin Iran da Amurka domin kawo ƙarshen yaƙi da magance sabanin da ke tsakani, ya isa Tehran in da ministan harkokin cikin gida na Iran ya tarbe shi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Wasu jami'ai sun nanata cewa kasancewar Asim Munir kwamandan sojojin Pakistan ba lallai ba ne yana nufin tabbatar da fahimtar juna kan tsarin farko ba.

Iran tana son a sanya batutuwa kamar kawo ƙarshen tashe-tashen hankula a yankin, 'yantar da kadarorin Iran da aka rike a ƙasashen waje, da kuma tabbatar da tsaron jiragen ruwan Iran a hanyoyin ruwa na duniya, a matsayin ginshiƙan tattaunawar.

…………………………………………..

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha