21 Mayu 2026 - 00:30
Source: ABNA24
Yakin Iran Ya Gurgunta Tattalin Arzikin Qatar

A Wata makala da jaridar New York Times ta fitar mai taken "Yakin Iran yana gurgunta daya daga cikin kasashe mafi arziki a duniya" ta yi nazari kan sakamakon yakin Iran, rufe mashigar Hormuz, da hare-haren kai tsaye kan abubuwan more rayuwa na makamashi na Qatar, ta kuma rubuta cewa tattalin arzikin wannan kasa mai arziki da ke gaɓar tekun Farisa ya shiga cikin mummunan taɓarɓarewa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Yakin bai kai hari kan masana'antar iskar gas na Qatar kadai ba, har ma ya jefa dukkan tsarin ci gaban kasar cikin koma baya mai tsanani; tsarin da aka gina a cikin shekaru talatin da suka gabata bisa kwanciyar hankali na yanki, jawo hannun jari na kasashen waje, yawon shakatawa na alfarma, da mayar da Doha cibiyar kasuwanci, sufuri, da abubuwan da suke faruwa na duniya.

Hare-haren rokoki kan rukunin makamashi na "Raas Lifan" da fitar da gargadin tsaro a Doha akai akai sun matuƙar raunana hoton da Qatar ta shafe shekaru tana ginawa a matsayin kasa mai kwanciyar hankali, aminci, da mafi dacewa don zuba jari.

Qatar, ba kamar Saudi Arabia da UAE ba, ba ta da wata hanya ta daban don kewaye ko maye mamadin mashigar Hormuz ba, kuma wannan lamari ya bayyana dogaro da tattalin arzikin kasar ga wannan hanyar ruwa mai mahimmanci. A cikin wannan yanayin, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Qatar zai fuskanci raguwa mai yawa a wannan shekara.

Qatar ba ta fuskanci durkushewar tattalin arziki ba saboda dimbin dukiyarta zuwa yanzu ba, amma yakin ya nuna cewa ko da daya daga cikin kasashe mafi arziki a duniya zai iya zama mai rauni cikin sauri a gaban rikicin yanki.

.........

Your Comment

You are replying to: .
captcha