Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Abdul Khaliq Abdullah, mai ba da shawara ga shugaban UAE, ya tabbatar da cewa ƙasarsa ba za ta kasance cikin duk wani haɗin gwiwa na soja da Isra'ila ba, kuma ba ta ɗauki wannan gwamnatin a matsayin amintaccuya abokiyar tarayyar ta ba.
Wannan ja da baya ya faru ne a daidai lokacin da cibiyoyin nukiliya na UAE a Al-Dhafra suka sha harin makamai, kuma Iran ta bayyana Isra'ila a matsayin wacce ta aikata wannan harin.
Kafin wannan, tona asirin tafiye-tafiyen sirri na Netanyahu zuwa Abu Dhabi ya jawo fushin UAE.
Har yanzu ba a san ko UAE ta gano rawar da Isra'ila ta taka a harin da aka kai wa ƙasarta ba, ko kuma tana so ta ja da baya don fuskantar fushin Larabawa da na.
...........
.......
Your Comment