Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A rahotannin da kafafen yaɗa labaran Isra'ila suka fitar, sojojin mamaya sun kama jiragen ruwa 41 daga cikin gwamman jiragen ruwa da suke awannan ayari.
Sojojin ruwan Isra'ila sun yi amfani da mahara na rundunar "Shaytet 13", sun kai hari kan ayatin jiragen Samoud na duniya a cikin ruwan kasa da kasa. Wannan ayarin da ya ƙunshi gwamman jiragen ruwa da daruruwan masu fafutuka na kasa da kasa, yana ɗauke da kayan agaji na jin kai zuwa zirin Gaza. Sai dai ta hanyar kai farmakin Isra'ila na ƙarshe, sun kame dukkan jiragen ruwan (ciki har da kwale-kwale 41 da aka kama da kwale-kwale 10 na Turkiyya da suka yi tsayin daka), tare da kama masu fafutukar.
Gwamman masu fafutuka na ayarin Samoud sun fara yajin cin abinci
Ayarin Samoud na duniya: Fiye da masu fafutuka 87, a matsayin nuna adawa da sace su da Isra'ila ta yi, da kuma nuna goyon baya ga fursunonin Falasdinu 9,500 da ke kurkukun wannan gwamnati, sun fara yajin cin abinci.
A karo na biyu a cikin makonni uku, sojojin Isra'ila waɗanda ke da'awar cewa su ne "sojoji mafi kyawawan halaye", sun sace abokan tafiyarmu a ruwan kasa da kasa.
...........
.......
Your Comment