19 Mayu 2026 - 12:03
Source: ABNA24
Mutane 4 Sun Mutu A Zanga-Zangar Adawa Da Hauhawar Farashin Man Fetur A Kenya

Ministan cikin gida na Kenya, Kipchumba Murkomen, ya bayyana cewa mutane huɗu sun rasa rayukansu a jiya Litinin a zanga-zangar da aka yi a garuruwa da dama na Kenya don adawa da hauhawar farashin man fetur sakamakon yaƙi da Iran, bayan da yajin aikin gama-gari a fannin sufuri na jama'a ya bar matafiya a makale.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa:  Kungiyar "Transport Sector Alliance" ta ce a ranar Lahadi da ta gabata motocin ƙungiyoyin da ke cikinta za su daina aiki daga tsakar dare don nuna adawa da wannan yunkurin, yayin da 'yan sanda suka ce za su ɗauki matakan da suka dace don tunkarar duk wani tashin hankali.

Murkomen ya bayyana a wani taron manema labarai da gidan talabijin: "Mun rasa 'yan Kenya huɗu a tashe-tashen hankulan da suka faru a yau, wadanda kuma suka janyo wa mutane sama da 30 raunuka." Hukumar kula da makamashi da man fetur ta Kenya ta ƙara farashin man fetur da kashi 23.5 cikin ɗari a makon da ya gabata - bayan ta ƙara kashi 24.2 cikin ɗari a watan da ya gabata - yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya rage isar da mai da iskar gas a duniya.

Kamfanonin zirga-zirga da ƙungiyoyin masu zanga-zanga daban-daban sun rufe hanyoyin da ke zuwa babban birnin Nairobi a safiyar litinin din don aiwatar da yajin aikin.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye a wasu yankuna, yayin da wasu masu zanga-zanga suka kona tayoyi don rufe manyan tituna, wanda ya ƙara tsananta cunkoso tare da barin matafiya da yawa a makale.

A Mombasa, babban birnin bakin teku na Kenya, yajin aikin ya haifar da fargabar cewa za a samu jinkiri a yanayin samar da kayayyaki.

Murkomen ya ce ministocin kuɗi, sufuri da makamashi za su gana da masu gudanar da sufuri na jama'a daga baya yau don tattauna hanyar magance rikicin, yayin da ministan kuɗi John Mbadi a farkon yau ya ce farashin da ake yi a halin yanzu akwai ma tallafin gwamnati a cikinsa.

Kenya tana shigo da dukkan kayayyakinta na man fetur daga Gabas ta Tsakiya ta hanyar yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin gwamnatoci da masu samar da kayayyaki daga yankin Tekun Farisa.

Kenya ta ƙara farashin man fetur a Nairobi zuwa shilling 214.25 (daloli 1.66) a kowace lita daga 206.97, da dizal zuwa shilling 242.92 daga 196.63 na tsawon lokacin daga 15 ga Mayu zuwa 14 ga Yuni, yayin da farashin kananzir ya tsaya a shilling 152.78 ba tare da canjawa ba.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha