13 Mayu 2026 - 10:10
Source: ABNA24
Hizbullahi Na Ci Gaba Da Barin Wuta Kan Sojojin Isra'ila

Wannan rahoton yana dauke bayanan ayyukan fagen daga na Hizbullah tun daga hare-haren jirage marasa matuka na 'Al-Naqoura' zuwa farautar tankar Merkava a 'Al-Tayyibah'

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar Musulunci ta Lebanon (Hizbullah) tun daga yammacin Talata har zuwa yanzu, ta hanyar fitar da sanarwoyin soji a jere, ta ba da rahoton aiwatar da jerin ayyuka na musamman da manyan hare-hare kan tarukan sojojin sahayoniya da kayan aikinsu a wurare daban-daban na kan iyaka.

Mayakan kungiyar Musulunci ta Lebanon, a lokuta biyu a jere, sun kai hari kan taron sojojin makiya sahayoniya a kusa da tashar jiragen ruwa ta 'Al-Naqoura'. An kai wannan hari ta hanyar amfani da gungun jirage marasa matuka na kunar bakin wake, wadanda suka kai hari ga inda aka nufa da cikakken nasara. 

A lokaci guda, wakilin Al-Mayadeen a kudancin Lebanon ya kuma ba da rahoton ci gaba da hare-haren rokoki da manyan bindigogi kan tarukan sojojin mamaya a wannan yanki.

Kungiyar Musulunci a cikin sanarwoyi guda biyu daban-daban ta bayyana cewa ta gano tare da kai hari ga wani jami'in sojan sahayoniya da ya kutsa a cikin wani gida yana mai garkuwa da shi a garin 'Al-Bayyadah'. An kai wa gidan hari a matakai biyu da jirage marasa matuka na kunar bakin wake na kungiyar, wanda ya haifar da hasarar rayuka a tsakanin sojojin makiya.

A cikin sa'o'i na karshe da yammar jiya Hizbullah ta Lebanon ta sanar da cewa mayakan kungiyar sun yi nasarar kai hari kan wati tankar Merkava ta sojojin sahayoniya a garin 'Al-Tayyibah' da makaman da suka dace (makamai masu sulke). A wannan aikin, tankar da aka ambata ta lalace gaba ɗaya kai tsaye.

.................

Your Comment

You are replying to: .
captcha