Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kungiyar ta faɗa a bayanin fatawar daga fitar cewa: Jihadi a Falasdinu da taimaka musu, wajibi ne na shari'a da nauyi ne na Musulunci da Larabawa da Ƴan Adamntaka.
Kuma yin shiru game da wannan cin zarafi da rashin fuskantar shi ta hanyar motsawar gwamnatocin da ke mulki da rundunonin soji na hukuma, daga mafi kusa zuwa mafi dacewa, haramun ne a shari'a. Kuma lalle barin Gaza, Masallacin Al-Aqsa, Kudus (Baitul Makdis) da Falasdinu a cikin kisan kare dangi da halaka, cin amana ne ga Allah da ManzonSa da kuma muminai, kuma yana daga cikin manyan zunubai da laifuffuka a wurin Allah Subhanahu.
................
Your Comment