11 Mayu 2026 - 00:22
Source: ABNA24
Sojojin Isra'ila Sun Tsere Daga Sansaninsu Don Tsoron Harin Hizbullah

Kafofin yada labarai na sahayoniyar sun ba da rahoton cewa sojojin rundunar sun bar wani sabon sansanin soji da aka kafa a kusa da iyakokin arewacin Falasdinu da aka mamaye, kwana daya kacal bayan da aka kafa shi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gidan talabijin na "Kan" ya bayyana cewa an kafa wannan sansanin ne kwanan nan da sojojin sahayoniyar suka zauna a cikinsa a kusa da iyakar arewa.

Kafofin yada labarai na Larabawa sun ba da rahoton kai nau'ikan hare-haren mayakan Hizbullah a arewacin Falasdinu da aka mamaye, a matsayin ramuwar gayya ga cin zarafi da laifukan da Isra'ila ke ci gaba da yi wa al'ummar Lebanon.

A cewar wadannan kafofin yada labaran wasu garuruwan da sahayoniyoyi ke zama a arewacin Falasdinu da aka mamaye sun fuskanci hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami na Hizbullah.

Hizbullah ta Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari kan wani taro na sojojin Isra'ila a garin Sir Hifa, ta hanyar amfani da jirgi maras matuki na kunar bakin wake.

Kungiyar ta kuma kai hari tare da lalata wata motar Hamer ta musamman da ake amfani da ita wajen ayyukan sadarwa na sojojin Isra'ila a wannan garin.

Hizbullah ta kuma sanar da cewa ta kai hari tare da lalata wata cibiyar umarnin soji da aka kafa na sojojin sahayoniyar a kauyen Al-Bayyadah.

Gidan talabijin na 13 na sahayoniyar, a cikin martani kan hare-haren quadcopter na Hizbullah, musamman na baya-bayan nan da suka kai hari kan motocin harba makamai da na'urar tsaro ta "Kubbar Karfe" (Iron Dome) tare da sojoji da kwararrun injiniyoyi gyaran na'urar, ta rubuta cewa wannan makami ne mai kisa wanda har yanzu ba mu da mafita don kare rayukan sojojin mu a gabansa.

Kafofin yada labarai na yahudawa sun bayyana cewa saboda fargabar kutsawar jirage marasa matuka daga Lebanon, an ji karar kararrawar gargadi a garuruwan da sahayoniyoyi ke zama na Yishuv da Hajosherim, wadanda suke a yankin Asba'ul Galili.

.......................

Your Comment

You are replying to: .
captcha