10 Mayu 2026 - 21:49
Source: ABNA24
Hizbullahi Ta Kai Hari Hedkwatar Sojojin Isra'ila Da Na'urar Tsaronsu + Bidiyo 

Hizbullah ta kai hari kan hedkwatar sojojin Isra'ila da na'urar tsaron Iron Dome

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullah ta kasar Lebanon ta ba da rahoton kai wani hari da jirgin sama mara matuki kan wata sabuwar hedikwatar sojojin Isra'ila da ke kudancin Lebanon. Hari ta faru ne kan wata sabuwar cibiyar rundunar sojin Isra'ila a garin Al-Bayadh. 

Sannan Hizbullah ta kai hari tare da lalata na'urar tsaro ta Iron Dome wanda harin ya faru sau biyu cikin nasara a harin farko ta kai hari da Lalata na'urar a hari na biyu ya sake kai hari kan sojojin da suka zo don gyara wannan na'urar. Wannan harin ana ɗaukarsa mai tsanani ga tsarin tsaron Isra'ila.

Jaridar Sahayoniya Ma'ario ta tabbatar a yau Lahadi cewa harin da jiragen sama marasa matuka na Hizbullah suka kai na'urar Iron Dome ba ta iya gano shi ba, wanda ta ce mummunan rauni ne ga sahihancin wannan tsarin tsaron na'urar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha