8 Mayu 2026 - 18:46
Source: ABNA24
Hakikanin Abinda Ya Faru Kwana Uku A Mashigar Hormuz Tsakanin Iran Da Amurka

Ana kai hari a Qeshm, har yanzu ba wanda ya san daga ina harin ya fito, sai ga Tel Aviv da gaggawa ta ce: 'Ba mu ne ba!' Wannan gaggawar da take neman wanke kanta, yana nufin matsiyaciyar ta tsorata! Saboda halin da take ciki bai zama kamar dā ba, kowane kuskuren hesabi zai iya tayar da dukan yankin!

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Abin da ya fi ban sha'awa shi ne shirun da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kasar da ta ke gab da murƙusuwa a ƙarƙashin ƙafafun Jamhuriyar Musulunci. Sun sani sarai cewa idan wuta ta kunno kai a Tekun Farisa, wurin farko da zai ƙone shi ne waɗannan hasumiyoyin gilashi da tattalin arzikin da ya dogara da manyan kantunan Larabawa a yankin

A gefe guda kuma a Amurka, wani ɗan jarida ya ba da labari ba a hukumce ba cewa Amurka ce ta kai harin, sannan kuma CENTCOM ta sanar a hukumance, amma da sauri ta ce ba su da niyyar yaƙi, suna cikin shiri don kāre kansu ne kawai!

Wannan shi ne dai tsoron ɓoye amma abin so! Irin wannan damuwa da wasiwasin da ke yawo a ɗakunan kwamandncin Washington da Tel Aviv a yau. Waɗannan shirun, waɗannan musuntawa da suka yi cikin gaggawa da shirun kafofin watsa labarai da na hukumomi na maƙiyi, wanda suke ta fitar da bayanai fiye da kowace sanarwa cewa maƙiya sun shiga cikin ruɗani da damuwa! Allah ya ƙara!

Ana haka sai ga tashar CBS ta ce: Hare-haren da aka kai wa jiragen ruwa na Amurka a daren yau (jiya) ya fi na kwanakin baya tsanani!'

Jiragen ruwan yaƙi na USS Truxtun da USS Mason sun fuskanci hari mai tsanani daga Iran. Jami'an Amurka sun bayyana harin a matsayin mafi tsanani da barna fiye da hare-haren da aka kai wa waɗannan jiragen 'yan kwanakin baya.

Jami'an Amurka sun ce kwale-kwalen Iran masu tsananin saurin gudu sun kai kusa da jiragen ruwan yaƙi wanda har sai da suka tilastawa jiragen amfani da bindigogin ruwa, na'urorin yaƙi na kusa, da makaman da aka sanya a saman benen jiragen. Iran a cikin wannan arangama ta yi amfani da jirage marasa matuƙa (drones) da makamai masu linzami.

Sojojin ta'addancin Amurka tare da haɗin gwiwar wasu ƙasashen yankin sun kai hari ta sama a gabar tekun Khamir, Sirik, da tsibirin Qeshm. A matsayin ramuwar gayya, an kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka a gabashin Mashigar Hormuz da kudancin tashar Chabahar hari, aka yi musu barna mai yawa...

Trump Ya Lalata Fujairah Ne Kawai Ya Koma Ba Ya Barsu Da Allah Ya Isa

Bari mu sake duba abin da ya faru a cikin kwanaki biyu ko uku da suka wuce cikin sauki da takaitawa:

Na farko, Trump ba zato ba tsammani ya sanar da cewa yana son ya buɗe mashigar Hormuz da ƙarfi ba tare da izinin Iran ba! Washe garin ranar bayan haka, sojojin ta'addanci na Amurka suka sanar da cewa za su auwatar da rakiyar soji don jiragen ruwa su wuce ta mashigar lafiya, kuma su karya ƙudurin Iran!

To, al'amari ya fara; jiragen ruwan Amurka suka fara aiki; yawancin jiragen ruwa (tashoshin jigilar kaya) tun da sun san yaudarar Amurka, ba su motsa daga wurinsu ba, ba su sadaukar da kansu ba saboda wannan takama. Duk da haka, jiragen ruwa guda ɗaya ko biyu waɗanda liassafinsu ya ɓace, sun yi ƙoƙarin wucewa, amma suka ƙone a cikin wuta!

A cikin wannan lokacin, Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi iƙirarin cewa an bankawa Fujairah wuta ta hanyar makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa. Ba a san ainihin daga ina hare-haren suka fito ba. Amma ko ta yaya ne ma Fujairah ta ci gaba da cin wuta!

Jiragen da suka saba dokoki sun ci wuta, Fujairah ta ƙone a wuta! Jiragen ruwan yaƙi sun makale a tsakiyar mashigar; ta yiwu sun tambayi junansu: Wai Shin me muka zo yi nan?'!

Trump da sauri ya sanar da gazawar aikin nasa; amma jiragen sun riga sun ƙone, Fujairah ta riga ta kama da wuta; kuma yanzu jiragen ruwan yaƙi sun makale. A daren jiya Trump ya yanke shawarar kubutar da jiragen ruwan yaƙi da suka makale; duk da haka, a kan hanyar komawa, sun fuskanci hare-hare masu tsanani daga sojojin ruwa na Iran.

Don haka dukan abin da ya faru shi ne: Jiragen ruwan yaƙi sun zo don bude mashigar Hormuz sun kasa, sun makale, sun gaza komawa; saboda mashigar ta kasance a hannun Iran da dakarunta!.

Your Comment

You are replying to: .
captcha