Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ministan harkokin wajen Spain José Manuel Álvarez ya sanar da cewa gwamnatin Sahyoniya ba ta bayar da wata shaida ba kan tuhume-tuhumen da ta yi wa masu fafutukar jiragen Samoud ba da ta tsare.
Spain tana hada kai da Brazil don daukar matakin hadin gwiwa kan gwamnatin idan ta ci gaba da tsare masu fafutukar a cikin ruwan kasa da kasa.
Isra'ila Ta Sake Kai Hari Da Ƙwace Wasu Jiragen Ruwa 4 Daga Jiragen Samoud.
Jami'an Ayarin Samoud da ke dauke da kayan agaji zuwa zirin Gaza sun sanar da cewa sojojin Isra'ila sun sake kai musu hari. Jaridar Al Jazeera ta ruwaito, tana mai ambatowa daga wadannan mutanen: jiragen sama masu saukar ungulu na Isra'ila da jiragen sama marasa matuka sun kewaye jiragen ruwa hudu na kawancen Samoud, kuma an ga jirgi daya da da ya kashe fitilunsa don kar a gane shi.
Your Comment