Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Da yake mayar da martani ga labarin wata babbar gobara a tashar mai ta Fujairah da kuma alakanta hakan ga sojojin Iran, wani jami'in soji ya ce Jamhuriyar Musulunci ba ta da wani shiri na shirin kai hari a wurin. Ya jaddada cewa abin da ya faru ya samo asali ne sakamakon yunkurin da sojojin Amurka suka yi na samar da hanyar da jiragen ruwa za su tsallaka wuraren da aka haramta wucewa a mashigar Hormuz, kuma ya zama wajibi sojojin Amurka su ɗauki nauyin wannan aika aika.
Jami'in sojin ya kara da cewa ya kamata jami'an gwamnatin Amurka su kawo karshen amfani da karfi a harkar diflomasiyya da kuma dakatar da kasadar soji a wannan yanki mai muhimmanci da ya shafi tattalin arzikin duniya.
Your Comment