Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kiyasin kudin da aka kiyasta, wanda ya hada da kudin sake gina cibiyoyin sojin Amurka da kuma maye gurbin kayan aikin da aka lalata, ya kusa dala biliyan 40 zuwa dala biliyan 50. A cewar CNN, hare-haren da Iran ta kai wa Amurka a yankin Tekun Farisa a farkon yakin sun lalata akalla sansanonin sojin Amurka tara cikin awanni 48 kacal kuma sun lalata sansanonin a Bahrain, Kuwait, Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar wanda su ba'a saka asarar kudaden gyara su ko mayar da mamadin kayan da ke ciki ba
CNN: Kiyasin dala biliyan 25 da wani babban jami'in Pentagon ya bai wa 'yan majalisa na jimillar kudin yaki da Iran abin takaici ne kuma bai hada da kudin gyara barnar da aka yi wa sansanonin Amurka a yankin ba.
Your Comment