23 Afirilu 2026 - 17:17
Source: ABNA24
Sabbin Damarmakin Da Gwagwarmayar Musulunci Ke Shi Rufe Mashigar Babul-Mandab 

Yamen za ta rufe mashigin Babul Mandeb ya zamo babu jirgin da ke iya wucewa idan matsin lambar Amurka ya karu ga Iran

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Idan aka yi la'akari da kawanyar da sojojin ruwan Amurka suka yi wa Iran da kera iyakar daren jiya na kwace wani jirgin ruwan Iran da sojojin Amurka suka yi, wanda hakan ya saba wa tsagaita bude wuta, mai yiyuwa ne nan gaba kaɗan fagen gwagwarmaya ya dauki sabon mataki na wani yanayi mai yuwuwa rufe mashigar Babul Mandeb na Yemen. 

Mashigar Babal-Mandeb na daya daga cikin muhimman kulli da mahada a harkar cinikayyar duniya. Wanda kusan kashi 10 zuwa 12% na man fetur a duniya kuma kusan kashi 10 zuwa 15% na kasuwancin teku na duniya yana ratsawa ta wannan hanya ne. Har ila yau, yana kan babbar hanyar Asiya-Turai, wanda ke da wani yanki mai mahimmanci na kayan yau da kullun na duniya, har zuwa kashi 25% na musayar teku ya dogara a mashigar ne. A gefe guda kuma Jakadan Somaliya a Habasha da Tarayyar Afirka ta tabbatar da cewa: Duk kasar da ta yi katsalandan a harkokin cikin gida na Somalia kuma ta lalata mutuncinta da ikonta na yankinta za ta fuskanci mummunan sakamako, ciki har da yiwuwar hana shiga mashigar Babal-Mandeb. Gwamnatin Somalia ta sanar da cewa za ta haramta wa jiragen ruwan Isra'ila ketare mashigar Babal-Mandeb a matsayin martani ga yadda gwamnatin Isra'ila ta amince da yankin "Somaliland" na 'yan aware.

Biyo bayan hakan an samu rahoton faruwar wani lamarin tsaro ga wani jirgin ruwan dakon kaya a gabar tekun Somalia mai nisan mil 83 kudu maso gabashin Somalia. Daya daga cikin hanyoyin da za a bi wajen tsallake tekun Bahar Maliya da Babul-Mandeb wanda idan aka rufe wannan mashigar to gudanar da kasuwanci sai dai ya bi tare da tsallaka hanyar Afirka, wanda kuma yana da matukar hadari da tsayi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha