Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sansanin IRGC na Hamzah Sayyidush Shuhada ya sanar a cikin wata sanarwa cewa, mayakan Islama sun kai wa maboyar 'yan kungiyar ta'addanci ta Demokradiyya hari a yankin Jijnkan da Balisan da ke yankin Kurdistan na Iraki.
A wannan harin an yi amfani da jirgi maras matuƙi sannan an tabbatar da mutuwar ƴan ta'adda uku daga cikin wadannan 'yan ta'addan tare da raunata wasu biyar.
Waɗannan ƴan ta'addan sun kasance daga cikin manyan masu aikata kisan gillar da aka yi wa Shahidi Mehdi Salmasi, daya daga cikin mayakan Furaja a shekarar 2017 a Piranshahr. Bincike da gano sauran 'yan ta'adda har yanzu yana kan ajandar sansanin IRGC na Hamza Sayyidush Shuhada.
Your Comment